Kungiyar Ci Gaban Yankin Funtuwa Ta Tallafa Wa Mutane 100 Da Kudade Don hidimar Sallah

  0
  983
  Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa da Imam Usama da Dan majalisar wakilai Muktari Dan Dutse a wajen taron kaddamar da kungiyar a Abuja

  Isah Ahmed Daga Jos

   A makon da ya gabata ne kungiyar ci gaban yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina, ta yi  wani gagarumin aiki a yankin. Inda ta tallafawa mutanen yankin  sama da 100 da kudade don, gudanar da hidimar babbar Sallah. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da shugaban kungiyar kuma Limamin masallacin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke  zone B, Apo babban birnin tarayya Abuja Imam Ibrahim Awwal [Usama]. Don jin abin da ya karfafa wa kungiyar gwiwar yin wannan aiki tare da ayyukan da kungiyar ta sanya a gaba. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:-

  GTK: Mene ne ya karfafa maku gwiwar kafa wannan kungiya kuma mene ne ayyukan wannan kungiya?

  Imam Usama: Babban abin da ya karfafa mana gwiwar kafa wannan kungiya shi ne domin kare mutuncin al’ummarmu tare da tallafa masu ta hanyoyi da dama. Kuma shekara daya kenan da kafa wannan kungiya. Kuma Sanata Abu Ibrahim daga Jihar Katsina da dan majaisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Funtuwa Honarabul Muktar Dan Dutse da Malam Hassan Idris da ni, muka tsaya wajen kafa wannan kungiya.

  Mai girma gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya kaddamar da wannan kungiya a Abuja. Kuma dubban mutanen wannan yanki suka halarci wajen kaddamar da wannan kungiya.

  GTK: Mene ne ayyukan wannan kungiya?

  Imam Usama: Ayyukan da wannan kungiya ta sanya a gaba sun hada da kula da mutanen mu masu rauni kamar marayu. Muna son mu gina gidan marayu da makaranta  da asibiti, domin mu rika tallafa masu muna daukar nauyinsu. Bayan haka za mu tallafa wa guragu da kafafuwan roba. Akwai wasu mutanen Indiya da muka yi magana da su kan wannan aiki. Haka kuma wannan kungiya za ta dauki nauyin yi wa jama’a masu ciwon ido aiki kyauta.

  Muna da bangarori daban-daban a wannan kungiya kamar bangaren lauyoyi, wanda ya kunshi lauyoyi, muna da su a  Abuja muna da su a Katsina. Idan kana cikin wannan kungiya wata shari’a ko rikici ya same ka, idan har kana da gaskiya za su tsaya su kwato maka hakkinka.

  Muna da bangaren kiwon lafiya wanda nan gaba idan har kana da katin shedar wannan kungiya za ka rika samun magani kyauta. Kuma muna da burin gina kananan asibitoci don amfanin ‘yan wannan kungiya. Kuma za mu gina makaratun yaki da jahilci don karantar da ‘yan wannan kungiya.

  GTK: Daga lokacin da aka kafa wannan kungiya zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne kuka samu?

  Imam Usama: Babbar nasarar da muka samu ita ce  wannan gagarimin aiki da muka yi na  tallafa wa  al’ummar wannan yanki na Funtuwa da kudade, don gudanar da hidimar babbar Sallah. Ganin halin da ake ciki na matsin rashin kudi, ya sanya wannan kungiya ta kudurin yin wannan aiki don wadanda aka tallafawa su gudanar da dawainiyar wannan babbar Sallah. A karkashin wannan shiri akwai wadanda aka bai wa kowane mutum Naira dubu 50 akwai wadanda aka bai wa kowanne mutum Naira dubu 30 akwai wadanda aka bai wa kowanne mutum Naira dubu 10. Sama da mutum dari ne suka sami wannan tallafi. Kuma mun tura wa wadannan mutane wannan tallafin kudade ne ta hanyar lambobin asusun ajiyarsu na bankuna da suka bamu.

  Mun yi wannan tallafi ne saboda ganin halin matsin da ake ciki. Uban wannnan kungiya  Mai girma Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtuwa Alhaji Idris Sambo Idris da al’ummar wannan yanki sun yaba da wannan kokari da wannan kungiya ta yi.

   Bayan haka  mun sami nasarar  samar wa matasan wannan yanki ayyuka da dama a wurare daban-daban.

  GTK: Mene ne babban burunku

  Imam Usama: Babban burinmu shi ne mu fitar da mutanenmu daga cikin kuncin rayuwa muna son mu ga mutanenmu suna cikin walwala da jin dadi. Kuma muna son mu gina yankinmu.

  GTK: Ko akwai wani tallafi da kuke samu daga wasu mutane don gudanar da ayyukanku?

  Imam Usama:  Gaskiyar magana lokacin da muka kaddamar da wannan kungiya, dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Funtuwa Honarabul Muntari Dan Dutse ya bamu kekunan Napep guda uku. Wadannan keke Napep an yi ta yin aiki da su ana tara kudin ana saka wa a asusun ajiyarsa, saboda lokacin ba mu bude asusun wannan kungiya ba.  A takaice dai har ya zuwa wannan lokaci ba mu samu mun karbi wadannan kudade da ake tarawa ba.

  Haka kuma  mai girma Sanata Abu Ibrahim ya bai wa wannan kungiya kyautar mota. Bayan haka a duk fadin Jihar Katsina, babu wanda ya dauki ko kwabo ya ba mu.

  Amma kamar wannan aiki da muka yi na tallafa wa ‘yan wannan yanki da kudaden yin hidimar babbar sallah, wasu Sanatoci da ‘yan majalisu da wasu mahimman mutane ne, suka tallafa wa wannan kungiya.

  GTK: Karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar wannan yanki?

  Imam Usama: Ina kira ga al’ummar wannan yanki kan kowa ya yi kokari ya zo ya shiga wannan kungiya. Domin wannan kungiya ta zo ne domin  taimaka wa  al’ummar wannan yanki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here