Shugaba Buhari Ya Amince Da Dakatar Da Okoi Obono-Obla

0
388

Daga Usman Nasidi, Daga Abuja

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da Okoi Obono-Obla, shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin kwato dukiyar gwamnati daga hannun ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati da suka yi sama da fadi a kan dukiyar ta gwamnati.

A cikin takardar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaba Buhari ya amince da dakatar da Mista Obono-Obla tare da umurtarsa ya mika kansa ga hukumar yaki da rashawa tsakanin jami’an gwamnati (ICPC).

Buhari ya dakatar da Mista Obono-Obla ne bayan an kai ruwa rana a kan batun zarginsa da karyar takardar karatu da kuma ragowar wasu laifuka masu alaka da cin hanci.

Takardar dakatar da Mista Obono-Obla, wacce Mista Mustapha ya saka wa hannu, ta nuna cewa Mista Dayo Apata, lauyan gwamnatin tarayya, zai ci gaba da jagorancin kwamitin kwato dukiyar gwamnati daga hannun masu handama da babakere.

Kazalika, takardar dakatarwar ta bayyana cewar ragowar mambobin kwamitin na nan daram a kan mukamansu, a saboda haka dakatar da Mista Obono-Obla bai shafe su ba.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa Mista Mustapha ya aika wa Mista Obono-Obla sakon ko ta kwana a kan ya zo ya karbi takardar dakatar da shi daga ofis. Ba a bude ofishinsa ba da safiyar ranar Litinin har zuwa rana, lokacin da wakilin jaridarmu ya ziyarci ginin da ofishin yake.

Alamun cewa akwai matsala tsakanin Mista Obon-Obla da fadar shugaban kasa sun fara fitowa ne ranar Juma’a bayan jami’an ‘yan sanda sun dira ofishinsa da ke unguwar Asokoro tare da rufe shi.

Wata majiya da ke da masaniya a kan harkokin bincike ta bayyana cewa an umarci jami’an tsaro su rufe ofishin Mitsa Obono-Obla ne don kar ya samu damar kwashe wasu kaya, musamman takardu, da za a iya amfani da su wajen tuhumarsa.

Ana zarginsa da tafka almundahana a aikin da aka ba shi na kwato kadarorin gwamnati daga hannun barayin gwamnati, lamarin da ya hana aikin ya yi wani tasirin kirki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here