Wadanda Suka Sace Fasto Sun Nemi  A Ba Su Miliyan Ashirin

0
381

Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna

WADANSU ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba da suka sace Limamin wata Coci mai suna Nagarta Baftis, Unguwar Makiri kusa da Udawa a karamar hukumar Chikun sun nemi a ba su kudi Naira Miliyan ashirin kafin kwanaki biyar.

Rabaran Elisha Noma ya shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne sati biyu da kashe wani Fasto Jeremiah Omolewa na Cocin Living Faith Unguwar Romi, Kaduna, an kuma biya kudi masu yawa kafin a saki matarsa daga hannun ‘yan garkuwa da mutanen.

Masu satar mutanen da suka zo dauke da makamai da akalla yawansu ya kai ashirin sun isa kauyen ne da misalin karfe daya da rabi na ranar Laraba suka kuma shiga da karfin tsiya cikin gidan Fasto din suka tafi da shi tare da dansa Emmanuel Elisha.

Amma daga baya sun saki dan nasa da barazanar lallai ya je ya samo naira Miliyan ashirin a matsayin fansar ubansa kafin kwanaki biyar ko kuma su kashe shi.

Lokacin da Emmanuel ke bayanin abin da ya faru ya ce ” akalla sun kai su ashirin kowannensu dauke da makami sun kuma zo kauyen ne suka fara dukan kofa babu wanda ya bude masu. Sai kawai suka shiga da karfin tsiya cikin gidan suka yi kaca-kaca da komai sun kuma tafi da wadansu abubuwan amfanin da suka ga suna so,da suka hada da wayoyin hannu da suturu a cikin akwatin uwata”. “Sun dauke ni tare da babana,amma bayan mun yi tafiya a cikin daji, sai suka sake ni suka tafi da babana. Daya daga cikin su a sanya kaya irin na sojoji.

“Lokacin da suka sake ni sun yi mini barazanar cewa idan ban kawo masu Miliyan ashirin ba nan da kwanaki biyar za su kashe shi. Ba mu kai wa ‘yan sanda rahoto ba saboda a can baya ma da muka samu matsala irin wannan da muka kai masu rahoto ba su yi komai ba, don haka muka ga ba amfanin kai masu rahoto”. Inji Shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here