‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Rabaren Cocin Nagarta Baptist A Garin Kaduna

0
351

Usman Nasidi Da Rabo Haladu, Daga Kaduna.

WASU ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake sace wani Fasto, Rabaran Elisha Noma na Cocin Nagarta Baptist da ke Angwan Makiri kusa da Udawa a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Hakan na faruwa ne makonni biyu bayan wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wani Faston Cocin Living Faith da ke Angwan Romi a Kaduna mai suna Jeremiah Omolewa sannan aka biya kudin fansa kafin suka sako matarsa.

‘Yan bindigan kimanin su 20 ne suka auka gidan Faston misalin karfe 1.30 na daren ranar Laraba suka yi awon gaba da shi da dansa.

Amma daga baya sun sako dansa, Emmanuel Elisha bayan sun masa barazanar cewa za su halaka mahaifinsa idan bai samo wani adadin kudi ba cikin kwanaki 5.

A cewar dan Faston, “Sun zo misalin karfe 1 na dare. Sun kai kimanin mutane 20 suka zo kauyen da suna ta buga kofofin mutane amma babu wanda ya bude musu. Daga nan sai suka fara aukawa gidajen mutane da karfi da yaji suna sace kayayakin mutane.

“Sun sace ni tare da mahaifina. Amma bayan wani dan lokaci a cikin daji sun sake ni amma suka tafi da mahaifina. Daya daga cikinsu yana sanye da kayan sojoji.

“Da za su sake ni, sun yi barazanar cewa za su kashe mahaifina cikin kwanaki biyar duk da cewa ba su fadi adadin kudin da suke so ba. Ba mu sanar da ‘yan sanda ba saboda a baya da hakan ya faru muka sanar da su babu abin da suka tsinana saboda babu amfani.”

A halin yanzu, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, DSP Yakubu Sabo bai amsa sakon da aka aika masa ba kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here