An Kama Matar Da Ta Kulle Yaro A Kejin Kare

0
422

Rabo Haladu, Daga Kaduna

‘YAN sanda a Legas sun kama wata mata da aka dauki hotonta tana cin zarafin wani yaro sannan ta kulle shi a wani keji na karnuka. Babu tabbas kan lokacin da aka dauki bidiyon amma an rinka yada shi a shafukan Twitter a farkon watan nan.

An ga matar a bidiyon, tana dukan yaron d a bel. Daga nan sai ta saka shi a wani keji ta rufe sannan ta kama gabanta. Akwai wasu karnuka biyu a cikin wani keji kusa da wanda ta saka yaron.

Bidiyon ya tayar da hankulan mutane a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi alkawarin bayar da lada ga duk wanda ya taimaka aka gano inda matar take.

A ranar Alhamis, mai magana da yawun ‘yan sanda, Dolapo Badmos, ta wallafa a shafin Twitter cewa an kama matar. Ta ce “Matar na hannun jami’an tsaro kuma za a gurfanar da ita a kotu. An kubutar da yaron, wanda maraya ne, kuma ana kula da shi a wani wurin mallakin gwamnatin Jihar Legas.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here