Idan An Inganta Sha’anin Noma A Duba Batun Tsaro Kuma.  Shugabar mata manoma.

0
590
Na Duke Tsohon Ciniki Kowa Ya Zo Duniya Kai Ya Taras
Rabo Haladu, Daga Kaduna
MANYAN manoma da ‘yan kasuwa a kasar nan sun fara mayar da martani game da kokarin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida, da ya sa shugaba Buhari ya ba shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele umurni da ya daina bai wa masu shigowa da kayan abinci daga kasashen waje tallafi.
Wannan ba shi ne karo na farko da mahukuntan kasar nan a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari za su dauki irin wanan mataki na hana a shigo da kayan abinci daga kasashen waje ba, domin daga hawansa mulki a shekara 2015 aka haramta shigowa da wasu kayayyaki 41 wadanda ake ganin ana samun su a cikin gida.
Shugabar Mata manoma a jihohin Arewa Bilkisu Mohammed ta ce wanan umurni yana da kyau sai dai ya bar baya babu zani, domin masu kama mutane su yi garkuwa da su sun hana mata yin noma. Sai ta yi kira ga shugaba Buhari da ya tashi tsaye ya yi maza maza ya magance harkar tsaro domin a ci moriyar wanan umurni, in ba haka ba zai yi wuya a ci nasara.
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu da aikin gona ta kasa Sanusi Maijama’a Ajiya ya ce umurnin yana da kyau sai dai ba lallai ne mutane su bi ba sai an dauki mataki, saboda sau tarin yawa manoma ba su samun tallafin da ake badawa domin su.
Kwararre a fanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya ce duk kasar da take so ta ciyar da kanta kuma a samu zaman lafiya dole ne ta dauki irin wannan mataki domin ta samu kudaden shiga daga kasashen waje saboda farfado da tattalin arzikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here