SHUGABAN riko na karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi Alhaji Babayo Sunuai Madara ya bada tabbacin jagorantar al’ummarsa bisa adalci.
Shugaban rikon ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabin karbar ragamar mulkin karamar hukumar daga hannun shugaban ma’aikatan karamar hukumar a sakatariyar karamar hukumar dake garin Azare jim kadan da rantsar da su.
Alhaji Babayo Sunusi ya kara da cewar, lokaci ya yi da zai tsaya kyam don ganin ya dawo da martabar karamar hukumar da take da shi a baya musamman wajen ganin al’ummominta na walwala da kuma gudanar da ayyukan raya kasa mai ma’ana ta yadda al’ummar za su amfana fiye da a baya.
Don haka ne ma ya bada tabbacin gudanar da mulkinsa bisa adalci ba tare da wariya kana ya kirayi al’umma da su ba shi cikakken goyon baya don ainahin komai ya tafi daidai.
Alhaji Babayo Sunusi ya kuma nemi al”ummar karamar hukumar Katagum da su ci gaba da halin da aka sansu da shi na masu bin doka da oda tare kuma da addu’ar Allah SWT ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da samu amfaninn gona mai yalwa a wannan damina ta bana.