Jihohin Arewa Maso Yamma Sun Yi Na Karshe A Jarabawar Fita Sakandare

0
542

Mustapha Imrana Abdullahi

IN ban da Jihar Kaduna da a jerin jadawalin sakamakon jarabawar da hukumar shirya jarabawar fita sakandare ta Afirka ta Yamma wato ( WAEC) ta fitar da Jihar Kaduna ta zo ta sha biyu sauran Jihohin Arewa Maso Yamma su ne na karshe’ a cikin jihohin tarayyar Nijeriya.

Hatta jihar da shugaba Muhammadu Buhari ya fito na can kasa a jerin sunayen jihohin kamar yadda sakamakon jarabawar ya nuna..

Jihohin irin su Abiya, Anambara,Edo,su ne suka zama zakaru wato masu kokarin da suka samu na gaba-gaba kamar yadda hukumar WAEC ta fitar da sakamakon shekarar 2018.

Yayin da Jihar Katsina ta zamo ta biyar daga can kasa sai ga jihohi irin su Jigawa, Zamfara da Yobe sun ci gaba da rike matsayinsu na kurar can baya da aka lissafa su a matsayin na uku daga can kasan sakamakon.

Jadawalin da hukumar shirya jarabawar WAEC ta fitar na dukkan jihohi 36 har da Abuja ya yi bayanin matsayin kowace jiha.

Kamar yadda jadawalin sakamakon jarabawar ya nuna Jihar Legas ce kadai da ta zo ta goma a jihohin yankin kudu maso yamma.

Jihar Kaduna kuma da ta zo ta sha biyu ta zama kan gaban jihohin yankin arewa maso yamma baki daya.

Jihar da yan ta’adda masu satar jama’a da shanu tare da yin fashi da makami ana yi wa matan aure zawarawa,‘yan mata fade kuwa wato, Jihar Zamfara da Jihar Yobe suka kasance a karshe baki daya.

Wadanda suka zamo na goma kuwa a jerin jadawalin sun hada da Abiya, Anambara,Edo,Ribas da Jihar Delta sai sauran Imo,Legas, Bayelsa, Enugu da Ebonyi.

Yayin da Jihohin Adamawa,Osun,Sakkwato,Bauci,Kebbi,Katsina,Gombe,Jigawa,Zamfara da Yobe Suka kasance na goma daga can karshe.

Ga dai yadda jerin jadawalin yake:-

 

Abia

Anambra

Edo

Rivers

Imo

Lagos

Bayelsa

Delta

Enugu

Ebonyi

Ekiti

Kaduna

Ondo

Abuja

Kogi

Benue

Akwa Ibom

Kwara

Ogun

Cross River

Taraba

Plateau

Nasarawa

Kano

Borno

Oyo

Niger

Adamawa

Osun

Sokoto

Bauchi

Kebbi

Katsina

Gombe

Jigawa

Zamfara

Yobe.

 

Kamar yadda hukumar ta fitar cikin yawan dalibai miliyan daya da dubu dari shida da suka zauna jarabawar a watanni Mayu da Yuni a shekarar 2019 a duk fadin Nijeriya, yawan dalibai 1,020519 da suka yi daidai da kashi 64.18 sun samu nasarar samun darussa biyar zuwa sama har da lissafi da turanci.

Kuma dalibai dubu 1,309,570 da suke zaman kashi 82.35 sun samu nasarar samun darussa biyar akalla wato dai da akwai darasin lissafi da turanci ko babu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here