Za Mu Kammala Aikin Kasafin Kudi Kafin Kirsimati – Ahmad Lawan

0
380

Mustapha Imrana Abdullahi

SHUGABAN majalisar Dattawan Nijeriya Alhaji Ahmad Lawan, ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin kammala duba kasafin kudin shekarar 2020 kafin lokacin bikin kirsimati na wannan shekarar.

Ahmad Lawan,ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Katsina jim kadan bayan ya gana da Gwamna da mataimakin Gwamnan Jihar Katsina a gidan gwamnati da ke jihar.

Ganawar da ta hada da Gwamna Aminu Bello Masari da mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu da kuma sauran jiga-jigan gwamnatin jihar an fara ta cikin nasara an kuma kammala tare da samun gagarumin ci gaban da ake fatar samu.

Shugaban majalisar Dattawan ya shaida wa manema labarai cewa ana sa ran bangaren shugaban kasa ya aika wa majalisar da kasafin kudin a cikin watan gobe na Satumba, ita kuma majalisar Dattawa ana sa ran ta kammala komai a game da kasafin kudin cikin watanni biyu daga lokacin da aka kai masu shi.

Ya ce irin yadda suke sa ran za su yi aiki mayar da Nijeriya ta zama ana yin kasafin kudi kamar can baya daga watan Janairu zuwa Disamba a kowace shekara.

Lawan, ya kuma bayar da tabbacin cewa za su gabatar da kudirin batun dokar man Fetur da Iskar Gas ya zama doka domin a samu canjin da ake bukata.

Ya kara da cewa majalisun tarayyar nan guda biyu za su yi aiki tare domin samar da ingantaccen ci gaba a bangaren aikin gona, Ilimi da kuma sauran bangarorin tattalin arzikin kasa baki daya.

Shugaban majalisar ya samu rakiyar shugabannin majalisar tare da Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu wato yankin Karaduwa Sanata Bello Mandiya da kuma na Katsina, Alhaji Ahmad Babba Kaita.

Shugaban majalisar ya shaida wa manema labarai cewa shi da tawagarsa sun kai wa shugaba Buhari ziyara a gidansa na Daura domin gaisuwar babbar sallah.

Baki daya bangarorin sun yi sallar Juma’a a masallacin Modoji da ke cikin garin Katsina.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here