Gwamnatin Nijeriya Za Ta Daukaka Kara Kan Cinta Tarar Dala Bilyan 9

0
421

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Najeriya ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami’ai da take zargi da hannu a wani hukuncin kotun Birtaniya da ya bukaci sai ta biya wani kamfani tsabar kudi har Dala Biliyan 9, saboda saba yarjejeniya da suka kulla.

Wata kotun London ce ta umarci gwamnatin Nijeriya a ranar Juma’a ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd (P&ID) wadannan makudan kudi ta hanyar kwace kadarorinta.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce batun tsohuwar shari’ah ce da jami’an gwamnatocin baya suka gaza wajen daukaka kara, har damar ta rufe.

“Masu mulki a wancan zamani ba su daukaka kara ba har kofa ta tsoshe,” in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin Buhari ta yi kokarin tunanin matakin da za ta dauka don jinkirta aiwatar da hukuncin domin bude kofar ta daukaka kara amma kotun a Ingila ta ce ba za ta bayar da wannan dama ba.

Ya zargi jami’an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira hadin bakinsu don a cuci Najeriya har suka bari abu ya kasance haka.

Ya ce duk da gwamnati za ta daukaka kara amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannunsa a cikin wannan hadin baki don a cuci Najeriya tare da wani kamfani na kasar waje, gwamnati za ta sa a kamo su kuma za  ta dauki mataki akansu.

Wata sanarwa a shafin intanet na kamfanin ta ce yarjejeniyar ta ba shi damar gina wata katafariyar masana’ntar gina sarrafa iskar gas wadda Najeriya za ta karba kyauta don bunkasa lantarki.

Amma kamfanin ya ce ya fuskanci karin kudin ruwa a kullum saboda rushewar yarjejeniyar, batun da lauyoyin gwamnatin  suka ce ya wuce hankali.

Tun farko a 2017 kotu ta bukaci Najeriya ta biya kamfanin kusan Dala Biliyan shida da rabi kafin yanzu kuma kotun London ta kara Dala Biliyan biyu da Miliyan dari hudu.

jimillar kudin dai ta kai kwatankwacin kashi 20 cikin 100 na dukiyar da Najeriya ta ce ta tara na lalitar kudadenta na kasashen ketare wato Dala Biliyan 45.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here