Hajiya Ummi El-Rufa’i Ta Shirya Taron Godiya Na Kwanaki A Garuruwan Kaduna

  0
  505

  Usman Nasidi, Daga Kaduna.

  DAYA daga cikin matan Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i wato, A’isha Ummi Garba El-Rufai, ta sake gode wa mutanen jihar da su ka zabi mai gidanta a matsayin Gwamna karo na biyu.

  Hajiya Ummi El-Rufai take cewa mutanen Kaduna ba za su ciza yatsa a game da sake zaben Gwamnan nasu ba. Mai dakin Gwamnan na APC ta ce gwamnatin nan za ta cika alkawuran da ta yi.

  A’isha Garba wato Ummi El-Rufa’i ta yi wannan bayani ne a cikin karamar hukumar Igabi inda ta fara wani taron gangami tana gode wa al’ummar jihar na sake mara wa APC baya a zaben da aka yi bana.

  Hajiya Ummi El-Rufai za ta shafe kwanaki hudu tana wannan zagayen gari. Yanzu dai matar Gwamnan ta shiga Yankin Jaji, Afaka, Rigachikun da Barakallahu da ke cikin Igabi.

  Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, shi ne ya tarbi mai dakin Gwamnan a gidansa da ke Rigachikun.Yusuf Zailani ya dauki lokaci ya yaba wa gwamnatin El-Rufai.

  ‘Dan majalisar na Igabi ya jawo hankalin gwamnatin APC da ta habaka harkar noma da kuma ba mata jari domin su fara kasuwanci tare da fadada wasu hanyoyi da kuma gina asibiti a garin Rigachikun.

  Matar Gwamnan ta cika alkawarin da ta yi na cewa za ta sake ziyartar wadannan wurare ta yi masu godiya da zarar APC ta samu nasara a zabe. APC ce ta kuma samu gagarumar nasara a Kaduna.

  A garin Jaji, Hakimin Rigachikun, Abdurrasheed Sani, da mutanensa sun ji dadin wannan ziyara da matar Gwamna ta kawo masu. Hakimin ya yi kira ga gwamnati ta duba kiwon lafiya da aikin yin matasa.

  A Unguwar Afaka, mai garin da kan shi, Sani Umar da wasu mutanensa ne suka tarbi Hajiya El-Rufa’i. Mutanen Afaka sun yaba wa gwamnatin jihar na ba da aikin hanyar Mashi Gwari zuwa Rigasa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here