YA NEMI HUKUMAR NDLEA TA BIYA SHI DIYYA

0
617
MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
SHEKARA biyu da jikkata shi a kokon gwiwarsa Alhaji Musa Shehu Yunusari,dan kasuwa dake garin fatakwal jihar Ribas ya bukaci hukumar da ke yaki da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma hana sha ta Nijeriya wato NDLEA ta yi masa adalci kana kuma ita gwamnati ta shigo cikin al’amarin a jinyar da yake fama da ita.
Alhaji Yunusari a zantawar da ya yi  da wakilinmu na kudanci ya yi zargin cewa
“ ka san shekarun baya kamar shekara biyu da suka wuce mun taso daga Fatakwal ni da wasu mutanen garin mu ,mu uku mun zo wani gari ana ce masa Guru sai jami’an hukumar NDLEA suka tare mu suna binciken kayanmu da suka tare mu suka samu kayan daya daga cikinmu da kayan laifi, wato daya daga cikin abokin tafiyar tamu sai suka kama shi suka sanya masa ankwa ,sai suka ce mana mu sauran fasinjan mota mu jira sai mota ta zo mu shiga mu tafi”.inji shi.
Dan kasuwar ya ci gaba da cewa “bayan sun tafi da yaron da suka kama can sai muka ga sun dawo tare da yaron, mu ji muke yi ma ko wani sako ne ma yaron zai bayar zuwa gidan su sai muka ji jami’an sunce muma mu sauko ai duk bakinmu daya ne,ni kuma na ce ai tafiya daya ce ta hada mu ba tare muke ba suka ce ai ba zai yiwu ba ai bakinmu daya ne, bayan da muka je ofis sai suka ce sai mun rubuta sitatiment wato jawabanmu mu amsa cewa da saninmu, tafiyarmu daya ce, ni kuma na ce ba zan je in rubuta
cewa da sanina ba saboda ba da sanina ba ne bama tafiyarmu daya ba, mota
ce ta hada mu”.
A cewar Alhaji Musa sai jami’in hulkumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi “Na ga ya dauko sanda ya tilasta min a kan sai lallai in ce da sanina ne, ni kuma na ce ban sani ba, ya  rika dukana da irin wannan sanda”.
Dan kasuwar ya kara da cewa sakamakon dukan da aka lakada masa sanadiyar jin mummunan rauni “ Sai da doke ni ta karkashin gwiwa ta kokon gwiwa da yake yawo sanadin dukan da aka yi mini a wurin ko yawo ba na iya yi, na je asibitoci da dama na je asibitin Damaturu na je na Guru har asibitin Gashuwa naje duk bai yiwu ba daga nan na tafi asibitn kashi na kasa da ke Dala Kano, wani babban lilkita da ya duba sai ya ce
wannan abin sakamakon sa abinda ya nuna wannan kokon gwiwar ne ya rabe
biyu ,don haka sai dai a yi maka aiki”. Ya bayyana lamarin da abin takaici ne da kuma rashin iya aiki.
Ya kara da cewa idan da akwai kwarewa a aiki da tund aya samu mai laifi da sai ya tafi da shi amma ba ya zo ya tursasa wa wanda bai-ji- ba-bai-gani ba, amsa laifin da bai aikata ba har ma ya yi masa rauni. Ya zuwa yanzu majinyacin ya ce ya kashe kudi domin neman lafiyar sa sama da Naira Dubu dari biyar  kuma ana bukatar wasu makudan kudin har Naira
Dubu dari uku domin yi masa aiki a asibitin kashi na Dala da ke Kano.Dukkanin jin tabakin wani jami’i na hukumar da ake zargi ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here