Yari Ya Nemi Kotu Ta Shiga Tsakaninsa Da Hukumar EFCC

0
302

Daga Usman Nasidi.

TSOHON Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari a ranar Juma’a ya kai korafi zuwa babbar kotun Abuja game da matakin da hukumar EFCC ta dauka na garkame masa gidansa da ke Maitama Abuja.

Yari wanda ya shigar da wannan korafin nasa ta hannun lauyansa Mahmud Magaji (SAN) ya ce garkame gidan da hukumar ta yi ya saba wa dokar shari’a.

Majiyarmu ta bayyana cewa babbar kotun Abuja a ranar Juma’a ta aminta da korafin hukumar ICPC inda ta rufe asusun bankunan Yari da ke Polaris da kuma Zenith Bank.

Magaji ta ce suna rokon kotu ta yi amfani da karfin da take da shi na shari’a wurin bai wa EFCC umarnin ta goge rubutun da ta yi da jan fenti a gidan gwamnan da ke Maitama.

Da yake bada misali ga wata matsala irin wannan, lauyan ya ce hukumar ba ta da ikon garkame gida haka nan kawai ba tare da samun izini daga wurin kotu ba.

Har ila yau, takardar korafin na dauke ne da bayanai cikin sakin layi 11 da kuma kwanan watan 16 ga watan Agusta, kamar yadda lauyan ya fadi.

“ Muna kyautata zaton wannan kotu mai adalci za ta duba korafinmu da idon basira.” Inji Magaji.

A wani labarin mai kama da wannan za ku ji cewa, kotu ta aminta da korafin ICPC inda ta kulle asusun bankin tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari.

Alkalin babbar kotun Abuja, Mai shari’a Taiwo Taiwo ne ya sanar da wannan hukuncin ranar Juma’a 16 ga watan Agusta inda ya umarci hukumar da ta wallafa labarin a jarida cikin sati biyu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here