Akalla Mutane 17 Aka Kashe A Kauyuka Uku A Katsina

0
397
Shugaba Buhari Da Gwamna Masari
Mustapha Imrana Abdullahi
RAHOTANNI daga jihar Katsina na cewa an kashe akalla mutane sha bakwai wadansu kuma sun samu raunuka daban-daban a wasu kauyuka uku.
Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana cewa an kashe mutane uku a Tsayau, da ke karamar hukumar Jibiya, sai guda sha daya a Dantakuri sai mutane biyu a kauyen Barza duk a karamar hukumar Danmusa.
 An dai kai wadannan hare haren ne a yammacin Lahadin da ta gabata tsakanin karfe bakwai na yamma zuwa karfe sha biyu na rana.
Kamar yadda mutanen kauyuka suka shaida wa majiyarmu maharan sun bata kayayyaki da dama sun kuma sace dabbobi da yawa.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar mana cewa mutanen kauyen da abin ya shafa har yanzu suna ta kokarin tantance asarar da suka yi tare da tabbatar da wadanda aka sace.
A kan haka ne wakilin mu ya samu tahoton cewa mutanen kauyen Tsayau sun yi wani gangamin jama’a suka kawo gawarwakin mutanen da aka kashe zuwa fadar sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman domin nuna fushin su a game da faruwar lamarin da yake faruwa a garuruwansu.
 Rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce da misalin karfe 15:30, wadansu mahara sun mamaye Tsayau da safe sun kuma yi abin gaba da shanu hudu.
 Mai rikon mukamin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ASP Anas Gezawa, ya ce “mutanen kauyen sun yi gangami inda suka bi maharan cikin daji da nufin su kwato shanunsu, sai maharan suka kara kashe mutane hudu daga cikin su nan da nan suka tsere cikin wani tsaunin Daji mai matukar duhu”.
Gezawa ya ce “suna shawartar jama’a a kodayaushe su rika kokarin bayar da cikakken hadin kai da goyon baya domin yin aiki tare da jami’an tsaro musamman idan lamari ya rutsa da masu satar shanu,satar mutane, ko masu kai hare hare irin fashi da makami da sauran ayyukan yanbTa’adda a cikin al’umma”.
 Har yanzu dai ana jiran jami’an tsaro su magantu a game da batun sauran hare haren a Kauyuka biyu da ke karamar hukumar Danmusa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here