Kungiyar Tuntuba Ta Arewa Ta Fitar Da Matsaya A Kan Karbar Karba

  0
  471
  Mustapha Imrana Abdullahi
  KUNGIYAR tuntuba ta Arewa wato (ACF) ta fitar da matsaya a kan tsarin karba-karbar mulki ga yankunan shiyyoyin kasar nan, inda suka ce batun karba-karba lamari ne da ya shafi jam’iyyun siyasa wajen fitar da dan takara daga kowace shiyya ta Nijeriya.
  Da yake tattaunawa da wakilin jaridar The Sun, babban Sakataren kungiyar Anthony Sani, ya ce kungiyarsu ta kalli batun a matsayin wani lamari ne na jam’iyyun siyasa domin ba tsarin mulki bavne, wani al’amari ne kawai na yarjejeniyar jam’iyyu in sun so yi.
  Sani ya ci gaba da cewa don haka babu wani ka-ce-na-ce game da wurin da shugaban kasa yakamata a fito a shekarar 2023, don haka wannan ya rage wa jam’iyyun siyasa su dauki matsayar da suka ga dama.
  “Don haka ya dace ‘yan Nijeriya su fahimci cewa siyasar inda mutum ya fito ba tsarin mulki ba ne wani tsari ne kawai na yarjejeniya a tsakanin jama’a da suke cikin jam’iyyu kawai, to ta yaya cikin yan takarar shugaban kasa da suka nemi kujerar shugabancin kasar nan a zaben da yagana daga cikin su 76, guda shida ne kawai suka fito daga arewa.
  “Kasancewa muna yin tsarin Dimokuradiyya mai jam’iyyu da yawa ya zama wajibi ga kowa ce ta Samar da tsarin samun nasarar ta”.
  “Don haka ban ga dalilin da zai hana a samu Jam’iyya ta fito da dan takarar ta daga bangaren kudancin kasar nan ba in har ta tabbatar da cewa wannan shi ne tsarin da za ta samu nasara”.
  “Duk jam’iyyar da yan kasa suka ce suna so kuma suka zabe ta a lokacin zabe in har daga kudu dan takarar ta yake kuma ta samu nasarar rinjaye kuri’un yan kasa, Shi kenan.Saboda ai irin wannan tsarin Dimokuradiyya ne ya sauke tsohon shugaba Jonathan da Bai samu nasara ba a zaben 2015”.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here