JABIRU A HASSAN, Kano.
SHUGABAN makiyaya na Dam din Kunnawa dake yankin karamar hukumar Dawakin Tofa Ardo Alhaji Geza ya ce za a sami ingantaccen zaman lafiya da karuwar arziki a kasar nan idan aka kammala shirin tsugunar da makiyaya na Ruga.
Ya yi wannan bayani ne cikin hirar su da wakilin mu yayin da Gaskiya Tafi Kwabo ta ziyarci Dam din Kunnawa inda makiyaya Duke zaune shekara da shekaru, inda ya kara da cewa ko shakka babu, tsugunar da makiyaya abu ne maikyau, sannan za’a sami zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya kamar yadda ake bukata.
Ardo Geza ya kuma yabawa kokarin da gwamnan jihar kano ,Dokta Abdullahi Umar Ganduje keyi wajen samar da guraren kiwo ga makiyaya a shirin nan na Ruga, sannan ya sanar da cewa tun da suke zaune a wannan guri basu taba yin rikici da manoman yankin ba, wanda a cewarsa, hakan abin alfahari ne kwarai da gaske.
Haka kuma shugaban makiyayan ya bayyana cewa dukkanin mutanen sa dake zaune a Dam din Kunnawa masu bin doka da oda ne, don haka nema suke da kyakkywar dangantaka tsakanin su da daukacin manoman wannan yanki kamar yadda ake gani.