Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Kebbi Ta Cafke Wani Mutum Da Ya Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 7 Fyade

1
499
 Kabir Wurma, Birnin Kebbi
RUNDUNAR ‘yan sanda a Jihar Kebbi a yau, ta cafke wani Ibrahim Umar a Kauyen Nufawa yankin gundumar Basaura a karamar hukumar Jega bisa ga ya yi wa wata yarinya mai suna Sadiya Muniru fyade a cikin duhun gero,
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Garba Mohammed Danjuma ne ya sanar da haka ga manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
 Danjuma ya ci gaba da cewa Ibrahim Umar ya amsa laifinsa a lokacin da ake tuhumarsa kuma ya tabbatar cewa bayan ya gama yin fasikanci da yarinyar ne sai ya ba ta biskit na Naira 25.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa rundunar ta kuma kama ‘yan ta’adda su goma sha ta kwas da suke addabar alumma a fadin jihar. Daga ckin laifuffukansu inji Kwamishinan sun hada da yin garkuwa da mutane, kissan gilla da kuma fasa shaguna.
Ya ci gaba da cewa da zaran yan sanda suka kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here