Al’ummar Musulmai A Gwarzo Sun Sami Karuwa

0
645

WANI bawan Allah wanda  aka fi sani da Ido da ke garin Lakwaya  ta karamar hukumar Gwarzo ya rungumi addinin musulunci ranar asabar din da ta gabata a wani kwarya-kwaryan taro da aka yi domin taya shi murnar shigarsa addinin gaskiya.

Shugaban majalisar karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama wanda  ya jagoranci karbar wannan bawan Allah da yanzu ake  kiransa da suna Nuraddeen ya bayyana matukar jin dadinsa dangane da abin da ya faru kuma a zamanin shugabancinsa, tare da yin fatan alheri gare shi da daukacin al’umar musulmi baki  daya.

Sannan ya yi alwashin cewa karamar hukumar Gwarzo za ta ci  gaba da kokari wajen kyautata wa  wadanda suka rungumi addinin na musulunci, tare da samar  masu da dukkanin ababen more rayuwa domin inganta  zamantakewar su, sannan ya bukaci al’umar musulmi da su rika tallaf wa mutanen da suka musulunta ta yadda za su fahimci cewa musulunci shi ne addini na gaskiya.

A karshe, Injiniya Bashir Kutama ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kafa gidauniyar Ganduje Foundation da ya yi tun  shekaru masu yawa wadda ta yi fice wajen musuluntar da maguzawa a fadin jihar Kano, don haka suma  suke  nasu  kokarin a matakin karamar hukuma.

Wakilinmu ya sami zantawa da wani hadimi ga shugaban karamar hukumar ta Gwarzo kuma jagoran matasa wato Kwamared Mustaoha Umar Tallo Gwarzo wanda  ya bayyana cewa shugaban karamar hukuma yana kokari wajen taimakon wadanda suka rungumi addinin musulunci tare da yi masu aiyukan alheri a gwamnatance da kuma aljihunsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here