El-Rufa’i Zai Fara Biyan Ma’aikatan Kaduna Sabon Albashi

0
404
Gwamna El-Rufa'i da mataimakiyarsa Hajiya Balaraba

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta sanar da fara biyan sabon karancin albashi na N30,000 daga ranar 1 ga watan Satumbar shekarar 2019, kamar yadda sanarwa daga fadar gwamnatin jihar, ‘Sir Kashim Ibrahim House’ ta bayyana.

Gwamnatin ta yanke shawarar fara biyan sabon albashin ne a karshen zaman majalisar zartarwar jihar da ya gudana a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta a karkashin jagorancin mataimakiyar Gwamna, Hadiza Balarabe.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne domin inganta walwalar ma’aikatan jihar, inda ta ce hakan ne ya sa tun a shekarar 2018 gwamnatin ta kafa wata kwamiti da za ta duba yiwuwar kara ma ma’aikata albashi.

“Muna duba karfin iya biyan albashin, da kuma karfin iya ci gaba da biyan albashin ba tare da yankewa ba, mun duba yadda jihar take tattara kudaden shiga da kuma kudin da take samu daga asusun gwamnatin tarayya.

“Aiwatar da sabon karancin albashi na kasa na N30,000 zai kara adadin kudaden da gwamnatin jihar Kaduna ke kashewa wajen biyan albashi da kashi 33, daga Naira Biliyan 2.82 zuwa Naira Biliyan 3.79, wannan kari na kusan Naira Biliyan 1 na nufin albashi da fansho zai kwashi kaso mai tsoka na kudaden jihar Kaduna.

“Don haka biyan wadannan makudan kudade, tare da kokarin samar da ababen ci gaba da more rayuwa na nufin karin nauyi a kan gwamnati na kara fadada hanyoyin neman kudaden shigarta.” Inji sanarwar.

Aiwatar da wannan sabon tsarin karancin albashi zai kara adadin albashin karamin ma’aikaci a jihar Kaduna da ke karbar mafi karancin albashi da kashi 67, yayin da albashin matsakaitan ma’aikata daga mataki na 10-14 zai haura da kashi 60.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here