Gwamnatin Najeriya Ta Fara Gudanar Da Gyare-gyare A Matatun Mai Guda 3

0
317

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR man fetir Najeriya, NNPC, ta kaddamar da fara gudanar da gyaran matatun man fetir na Najeriya, inda ta fara da babbar matatar mai da ke garin Fatakwal na jihar Ribas.

Shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin wani taron masana a harkar man fetir da ya gudana a jihar Legas a karshen makon watan jiya na Agusta, inda ya ce suna sa ran zuwa shekarar 2023 za su kammala gyaran matatun mai gaba daya.

Kyari ya koka game da yadda Najeriya ta kasance kasa mai dimbin arzikin man fetir, amma kuma ta buge da sayo mai daga kasashen waje, sai dai ya danganta hakan ga lalacewar matatun man fetir a Najeriya da ya sa ba sa iya samar da mai.

“Don haka muna bukatar karin zuba jari don ciyar da harkar man fetir gaba a Najeriya, da wannan ne ya sa zan yi iya bakin kokarina a matsayina na shugaban NNPC don ganin na tayar da komadun matatun man Najeriya na Warri, Fatakwal da Kaduna domin su samar da litar mai 445,000 a duk rana.

“Hakazalika muna aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu da ke kokarin samar da kananan matatun mai a Najeriya, bugu da kari za mu bayar da dukkanin gudunmuwa ga kamfanin Dangote da ke gina katafaren matatar mai da za ta samar da lita 650,000 na tataccen mai a duk rana.

“Burina shi ne naga Najeriya tana fitar da tataccen man fetir zuwa shekarar 2023.” Inji shi.

Daga karshe shugaban NNPC ya yi kira ga gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, wanda hakan zai rage makudan kudaden da gwamnati take kashewa a fannin, sa’annan ya nemi majalisar dokokin Najeriya ta kammala aiki a kan dokar masana’antar man fetir PIGB, don ta fara aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here