Sarkin Zazzau Ya Gabatar Da Bukatar Zazzagawa Ta Musamman Ga Buhari

0
1664
Shugaba Buhari A Yayin Ziyararsa A fadar Sarkin zazzau Shehu

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MAI martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wurin magance kallubalen da ke hana Asibitin Koyarwa ta Ahmadu Bello ABUTH da ke Zariya gudanar da ayyukanta kamar yadda suka dace.

Alhaji idris ya yi wannan kirar ne yayin da yake tarbar shugaban kasar da ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Zariya kwanakin baya a hanyarsa ta zuwa kaddamar da aikin ruwa na Zariya da gwamnatin Kaduna da hadin gwiwan wasu suka kammala.

Sarkin ya ce: “ABUTH tana daya daga cikin tsofaffin asibitocin koyarwa a kasar nan kuma tana da kwarrarun ma’aikata. Amma rashin isasun kudade da sauran kayan aiki na kawo cikas ga asibitin. A kan hakan ne yake rokon mai girma ya saka baki a batun.”

A kan kaddamar da aikin ruwan kuma, Alhaji Idris ya ce ya yi imanin cewa batun matsalar ruwa a Zariya zai zama tarihi. Ya shawarci shugabanni su zama masu hangen nesa musamman wurin samar da tsaro da rage talauci.

Alhaji Idris ya kuma bukaci shugaban kasar ya bayar da muhimmanci wurin farfado da masana’antun da suka durkushe a Kaduna tare da sake gina tittunan Zariya-Pambeguwa, Kaduna-Jos da Zariya-Funtuwa.

A bangarensa, Buhari ya tabbatar wa Sarkin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin magance kallubalen tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here