Ba ‘Yan Sanda Ne Suka Kubutar Da Mu Ba – Dalibin ABU

0
340
Shugaban Rundunar Yan Sandan Najeriya Muhammad Adamu

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

DAYA daga cikin daliban jami’ar ABU Zariya uku da ‘yan bindiga suka sace ranar Litinin a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya bayyana cewa babu hannun rundunar ‘yan sanda a cikin kubutar da su, kamar yadda rundunar ta yi ikirari kuma kafafen yada labarai suka yada.

A daren ranar Laraba ne rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kubutar da daliban jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, bayan wasu ‘yan bundiga sun sace su ranar Litinin a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a bangaren kafafen sadarwa na zamani, ya ce ya yi nadamar yada labarin cewa rundunar ‘yan sanda sun kubutar da daliban uku.

Da yake bayar da hakuri tare da janye maganar cewa ‘yan sanda ne suka kubutar da daliban, Bashir ya ce daya daga cikin daliban ne ya sanar da shi babu hannun rundunar ‘yan sanda a cikin maganar kubutar da su.

Da yake kare kansa, Bashir, ya ce ya yada labarin a shafinsa na Tuwita ne saboda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ne ya fara wallafa labarin cewa ‘yan sanda sun sanar da cewa sun kubutar da daliban uku; Aisha, Fatima da Umar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here