Gwamnatin Tarayya Da Gwamnatocin Arewa Su Samar Wa Matasan Arewa Ayyukan Yi-Alhaji Bello

  0
  496
  Alhaji Muhammad Bello

  Daga Isah  Ahmed, Jos

  WANI dan kasuwa da ke zaune a garin Jos fadar jihar Filato Alhaji Muhammad Bello ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnatocin jihohin arewa kan su yi kokari su ceto matasan da suke arewacin Najeriya ta hanyar samar masu da ayyukan yi. Alhaji Muhammad Bello ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce lallai ya kamata gwamnatin Buhari da gwamnatocin jihohin arewa su tallafa wa matasan arewa wajen samar masu da ayyukan yi, musamman idan aka yi la’akari da irin rawar da suka taka wajen zaben gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin arewa.

  Ya ce a  arewa akwai matasa da dama da suka kammala karatu amma ba su sami ayyukan yi ba, baya ga dimbin matasan da ba su sami zuwa makaranta ba.

  ‘’ Don haka muna  tunatar da shugaban kasa Buhari da mukarrabansa da ‘yan majalisun dattawa da ‘yan majalisun wakilai da gwamnatocin jihohin arewa kowa ya ba da gudunmawarsa,  a samarwa da matasan arewa ayyukan yi. Matukar matasan arewa suka sami ayyukan yi, za a magance matsalar ta’addanci da take damun arewacin Najeriya, na Boko haram da garkuwa da mutane  da rikice rikicen kabilanci da addini’’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here