Daliban Jami’ar Bayero Kano Sun Kirkiri Gawayi Mara Hayaki

0
348
Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU dalibai uku a Jami’ar Bayero a Kano sun kirkiro wata fasaha ta samar da gawayi wanda ba ya hayaki.
Suna hada gawayin ne ta hanyar amfani da sharar gona wadda bayan an girbe ake bari a gona irin su karare da su buntun shinkafa wadanda ba su da amfani sosai ga manoma.
Suna sayen sharar ne kan kowane kilo sai su karba su kai masana’antarsu inda ake sarrafawa.
Matasan dai sun hadu ne a wajen taro inda suka tattauna yadda za su kirkiro wannan fasahar.
Da aka bude wata gasa ta kasar Ingila a Jami’ar Bayero, sai suka kirkiro fasahar sannan aka hada musu ita a Cibiyar Kyankyasar Fasaha da ke Kano, Technology Incubation Centre.
Bayan an hada fasahar, sai suka halarci wannan gasar inda suka yi na daya, wanda hakan ya ba su damar zuwa birnin tarayya Abuja inda aka yi gasar yanki ta kasashen Afirka, kuma suka sake zuwa na daya.
Don haka suka samu zuwa Ingila inda suka halarci wani shirin bunkasa da horar da mutane masu fasaha.
Yanzu haka daya daga cikinsu ya koma Ingila inda idan suka yi sa’a zai ba su damar shiga cikin tawagar mutum shida da za su je Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amurka, domin gabatar da fasaharsu. Idan suka yi dace za su iya samun goyon bayan da zai bai wa mutum 10,000 damar samun aikin yi nan da shekara 10.
Mata da yawa a Afirka suna fama da cututtuka ko suna mutuwa sakamakon hayakin da suke shaka wajen girke-girke.
Hakazalika, sare bishiyoyin da ake yi wajen samar da gawayin itace na daya daga cikin dalilan da ke janyo kwararowar hamada da sauyin yanayi.
Da wannan tunanin ne, tawagar daliban mai suna Brycoal ta ga wannan fasahar ta dace wajen bayar da tasu gudunmuwa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here