JABIRU A HASSAN, Daga Kano
SHUGABAN karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya ce majalisar karamar hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga al’umar yankin domin ganin kowane bangare ya sami ribar dimokuradiyya bisa jagorancinsa.
Ya yi wannan bayani ne yayin da al’umar garin Gobirawa suka kai masa ziyarar godiya saboda aikin gyaran hanyar garin da ake yi masu, tare da jaddada cewa akwai aikace-aikace masu yawan gaske da karamar hukumar take yi domin inganta rayuwar al’uma ba tare da nuna kasala ba.
Sannan ya nunar da cewa majalisar karamar hukumar Gwarzo tana gudanar da wasu muhimman ayyuka wadanda kuma za su amfani al’umar yankunan da ake yin su kuma bisa la’akari da bukatun kowane sashe na fadin karamar hukumar, inda daga karshe shugaban ya yi godiya ga al’umar garin na Gobirawa saboda kaunar da suke bai wa karamar hukumar.
Haka kuma tawagar garin na Gobirawa ta ziyarci jagoran kungiyar Kano ta arewa ina mafita kuma mai yin sharhi kan al’amuran matasan Nijeriya Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo inda nan ma suka nuna godiyar su bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban karamar hukumar ta Gwarzo kamar yadda ake gani tare da jaddada goyon bayan su ga majalisar karamar hukumar Gwarzo bisa shugabancin Injiniya Bashir Abdullahi Kutama.
Da yake tsokaci dangane da wannan ziyara da mutanen garin Gobirawa suka kai masa, Kwamared Mustapha Umar Tallo ya ce shugaban karamar hukumar Gwarzo yana da manufofi kyawawa wajen bunkasa wannan yanki, sannan ya jaddada cewa majalisar karamar hukumar ta Gwarzo za ta cimma nasarar aiwatar da ayyuka a kowane fanni na zamantakewar al’umma ba tare da nuna banbanci ba.
Wata Gada Da Karamar Hukumar Gwarzo Ta Gyara.