
Daga Z A Sada
‘YAN jam’iyyar Conservative mai mulkin Birtaniya da na bangaren adawa sun kayar da gwamnatin kasar a mataki na farko na kokarin da suke yi na hana Birtaniya ficewa daga Tarayyar Turai ba tare da yarjejeniya ba.
Majalisar ta gudanar da zabe inda masu goyon bayan ta karbe ikon gudanarwa suka kayar da masu goyon bayan Firayiministan da kuri’u 328, inda ya sami 301.
Wannan na nufin za su iya gabatar da kudurin doka da zai jinkirta ranar ficewar Birtaniya daga Tarayyar ta Turai.
Amma Firayiministan ya fusata da matakin da ‘yan majalisar suka dauka, kuma ya yi alkawarin gudanar da wani kudurin a yi zaben gama-gari.