‘Yan Najeriya Za Su Kaurace Wa Hulda Da Kayayyakin Afrika Ta Kudu

0
348

Daga Z A Sada

‘YAN Najeriya da dama sun dade suna ce-ce-ku-ce da kiraye kiraye kan kaurace wa amfani da kayayyakin Afirka ta Kudu sakamakon kin jini da wasu ‘yan Afrika ta Kudun ke nuna wa ‘yan Najeriyar da sauran kasashe mazauna can.

Akwai kamfanonin Afirka ta Kudu da ke zaune a Najeriyar kamar kamfanin sadarwa na MTN da kuma shagunan saye da sayarwa na Shoprite da kuma kamfanin talabijin na DSTV.

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da kiraye-kiraye a shafukan sada zumunta musamman Twitter da Facebook inda suke nuna bacin ransu kan yadda wadannan kamfanonin mallakar Afrika Ta Kudu ke samun kudi da ‘yan Najeriya, amma wasu ‘yan kasar ke nuna kin jini da kuma kai hari ga ‘yan Najeriya mazauna kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here