Babban Dan Sanda 1 Ya mutu, 3 Sun Samu Rauni Bayan Kama Yaran Wadume

0
388

Daga Usman Nasidi.

WANI babban dan sanda daya mai mukamin ‘Insifekta’ ya mutu a daren ranar Litinin yayin da wasu hudu suka samu raunuka bayan motar jami’an tsaron ‘yan sanda na rundunar IRT (Intelligence Response Team) ta yi hatsari a kan hanyar Wukari a Ibi da ke jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne yayin da jami’an ‘yan sanda ke tafiya a motarsu kirar ‘Toyota Hiace’ a hanyarsu ta dawo wa daga kamen wasu da ake zargin suna da alaka ta kusa da babban mai garkuwa da mutanen nan da aka kama, wato Alhaji Hassan Bala (da aka fi kira Wadume).

Tawagar ‘yan sandan mai jami’ai guda takwas a karkashin jagorancin ASP James Bawa ta gamu da tsautsayin ne a kan hayarsu ta zuwa Wukari bayan sun kama masu laifin da ake zargin na da alaka da Wadume.

Rahotanni sun bayyana cewa motar da jami’an tsaron da masu laifin ke ciki ta yi hatsari ne sakamakon fashewar daya daga cikin tayoyinta, lamarin da ya sa motar ta kayar da su.

Rahotanni sun bayyana cewa wani jami’in dan sanda da aka bayyana sunasa da Clement ya mutu nan take, yayin da ragowar jami’an ‘yan sanda da masu laifin suka samu raunuka.

Kazalika, jaridar ta ce an kawo wa mutanen cikin motar agaji kuma an garzaya da su zuwa asibiti mafi kusa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya tabbatar da faruwar hatsarin ga jaridar, amma ya ce bai samu isassun bayanai a kan abin da ya faru ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here