Gwamna Bala Muhammad Ya Kai Ziyarar Ta’aziyyar Wasu Rashe-rashe

0
460
Mustapha Imrana Abdullahi
MAI girma Gwamnan jihar Bauci Sanata Bala A. Muhammad CON,  ya je gaisuwan ta’aziyya ga iyalai daban-daban a cikin garin Bauci domin yi masu gaisuwar rashin da aka yi. Ga dai gidajen da ya kai gaisuwar tare da sunayen wadanda suka rasun kamar haka:-
1- Gidan Marigayi Alhaji Muktari Ladan, ta’aziyyan rasuwar Hajiya Yalwa Tula.
2- Gidan sarkin kasuwar Bauci, ta’aziyyar rasuwar Alhaji Sunusi Adamu.
3- Gidan Alhaji Sani Toro, ta’aziyyar rasuwar matarsa Hajiya A’isha Sani Toro.
4- Ya halarci sallar jana’izar rasuwar mahaifiyar tsohon kakakin majalisar jihar Bauci Alhaji Abubakar Faggo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here