Mun Cire Shingayen Jami’an Tsaro A Kan Hanyar Abuja Da Birnin Gwari – El-Rufai

0
347

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jahar Kaduna ta sanar da kawar da duk wasu shingayen ababen hawa da jami’an tsaro suke kula dasu a kan manyan hanyoyin Kaduna zuwa Abuja, Kaduna zuwa Zaria da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Kwamishinan cikin gida na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Satumba, inda yace ana sanar da mutane su ankara cewa babu wasu jami’an tsaro dake tare hanya a wadannan hanyoyi 3.’

Don haka matafi su ankara, kuma kada su yi biyayya don tsayawa a duk wani shingen binciken ababen hawa da suka tarar a kan wadannan hanyoyi, haka zalika duk wanda aka kama yana tare motoci da sunan shingen bincike suna yi ne bisa haramci, kuma za’a hukuntasu.

“Majalisar tsaro ta jahar tana tabbatar ma jama’a cewa hukumomin tsaro na jahar suna gudanar da aiki tukuru don tabbatar da sun kawo karshen ayyukan yan bindiga a kan wadannan hanyoyi.

A duk inda aka ci karo da wani shinge, a kira cibiyar tsaro ta jahar Kaduna ta lambobi kamar haka: 09034000060 08170189999.” Inji sanarwar.

Daga karshe kwamishinan harkokin cikin gida na jahar Kaduna ya yi kira ga jama’a da su cigaba da lura da unguwannin da suke, sa’annan su tabbata sun sanar da hukuma aukuwar duk wani lamari da ka iya tayar da hankula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here