An Sace Gangar Mai Miliyan 22  A Jihar Edo

0
413
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNAN jihar Edo Godwin Obaseki, ya ce, cikin watanni shidan farko na wannan shekara, barayin mai sun sace gangar mai miliyan ashirin da biyu.
Gwamna Obaseki ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbata sun yi duk abin da zai yiwu wajen ganin an dakile matsalar satar danyen mai a kasar nan.
Godwin Obaseki wanda shi ne shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar kula da tattalin arziki ta kasa kan dakile matsalar satar danyen mai, ya ce, lamarin ya yi munin gaske da ya kamata kasar nan ta dauki mataki don shawo kan matsalar.
A cewarsa, matukar ba a dauki matakin dakile lamarin ba, to kuwa ko shakka babu, kasar nan za ta yi asara fiye da wanda aka gani a baya, a nan gaba. Gwamnan na jihar Edo yana wannan jawabi ne wajen taron masu ruwa da tsaki da kamfanin mai na kasa (NNPC) ya shirya a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here