Dan Majalisa Lawan Shehu Ya Jajenta Ga Wadanda Ruwa Ya Yi Wa Ta’adi

0
410

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

DAN majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Alhaji Lawan Shehu ya isar da sakonsa na ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar ambaliyar ruwa da kuma wadanda suka rasa gidaje a fadin karamar hukumar ta Bichi da jihar Kano da kuma kasa baki daya.

Ya isar da sakon ne ta hannun hadiminsa Malam Garba Sadah Bichi, inda  kuma ya yi fatar Allah Ubangiji ya jikan wadanda suka rasu ya bai wa iyalansu hakurin jure wadannan rashe-rashe da aka yi, tare da fatan Allah ya bai wa wadanda rushewar gidaje ikon sake gyarawa nan gaba.

Alhaji Lawan Shehu ya kuma yaba wa kokarin gwamnatin jihar Kano bisa  jagorancin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje na kyautata rayuwar al’ummar jihar ba tare da nuna banbancin siyasa ko na ra’ayi ba, inda  kuma ya jaddada cewa zai ci gaba da wakilci na adalci ga al’ummar karamar hukumar Bichi ba tare da gajiyawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here