Za A Kafa Tashoshin Manyan Motoci Na Zamani  A Duk Fadin Kasar Nan

0
539
Rabo Haladu Daga Kaduna
 WASU karin jihohi a kasar nan sun amshi zabin ware fili don kafa tashar zamani ta tsayawar manyan motoci don rage hatsari da samun kudin shiga.
Biyo bayan cimma yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya da hukumar shiga yarjejeniya da sassa masu zaman kan su “Concesion Regulatory Commission” kan kafa tashoshin zamani na tsayawar manyan motoci, yanzu an samu karin yankunan da suka aza harsashin kafa tashar.
Irin wadannan tashoshin dai na da tagomashi a kasashe masu ci gaban masana’antu, inda a  wasu garuruwan kan manyan hanyoyi kan zama a cunkushe da manyan motoci da kan dakata don hutawa da hakan kan toshe manyan hanyoyi.
Misalan biranen da direbobin manyan motocin kan tsaya sun hada da Obolo-Afor a jihar Enugu, Potiskum a jihar Yobe, Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Marabar Jos da ma Dikko a Neja, inda kwanan nan wata tankar mai ta kama da wuta har aka samu asarar rayuka.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya aza harsashin gina irin wannan tasha a garin Potiskum da kullum akalla manyan motoci 400 ke shiga da fita daga garin.
Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa, Hassan Bello, da hukumarsa ke jagorantar aikin, ya ce baya ga rage hatsari, tsarin zai samar da tsaro ga kayan da aka yi oda.
Duk da yunkurin dawo da titin dogo, har yanzu kashi 90% na kayan da akan yi oda a raba birane da kauyuka, manyan motoci ke kaiwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here