Barcelona Za Ta Sakar Wa Messi Mara, Neymar Na Tsaka Mai Wuya

0
431

Daga Z A Sada

Lionel MessiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

KULOB din Barcelona zai kyale Lionel Messi ya kama gabansa idan kwantaraginsa ya kare a lokacin bazara, amma fa sai idan dan wasan dan Argetina mai shekara 32 ya so yin hakan, kamar yadda aka yi yarjejeniya da shi a kwantaragin tasa. In ji jaridar (El Pais, via L’Equipe)

Za a bar Messi ya sama wa kansa kulob din da yake so daga ranar 1 ga Janairun 2019 – (Marca – in Spanish)

Ita kuwa jaridar (Sport – in Spanish) cewa take Real Madrid za ta baza komar zawarcin dan wasan Paris St-Germain na gaba Kylian Mbappe, mai shekara 20, a lokacin bazara.

Paris St-Germain dai ta gargadi Barcelona dangane da aniyar Real Madrid ta bukatar Neymar, mai shekara 27, a lokacin bazarar, in ji (Sport – in Spanish)

Za a matsa wa Neymar dan kasar Brazil lamba ya ci gaba da taka leda a PSG har sai ya rage yawan albashin da yake nema in ji shugaban gasar La Liga, Javier Tebas. Kamar yadda (Mail) ta rawaito.

Shi kuwa dan wasan baya dan kasar Ingila mai shekara 29, Chris Smalling na shirin yi wa Manchester United tutsu bayan da ya koma Roma, kamar yadda jaridar (Mirror) ta rawaito.

Manchester City ta kammala yarjejeniya da kulob din FK Cukaricki na kasar Serbia domin sayen Slobodan Tedic mai shekara 19 a watan Janairu, in ji (Manchester Evening News).

D’Margio mai shekara 17 wanda da ne ga tsohon manajan Manchester City kuma dan wasan gefe na Ingila, Shaun Wright-Phillips, ya rattaba hannu kan kwantaragin fara wasan kwararru a kulob din na Man City, kamar yadda jaridar Manchester Evening News ta rawaito.

Manajan Manchester City din, Pep Guardiola ya yi watsi da damar sayen dan wasan Barcelona, Philippe Coutinho, kafin dan wasan mai shekara 27 ya koma Bayern Munich, in ji (Marca – in Spanish).

Tsohon manajan Manchester United, Sir Alex Ferguson ya yi kokarin jan hankalin tsohon dan wasan Ingila na gaba, Michael Owen wajen taka leda da kulob lokacin yana matashi kafin ya je Liverpool, in ji jaridar (Mail).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here