Mata Mai Shekara 73 Ta Haifi Tagwaye Bayan Shekaru 57 Da Aurenta

0
377

Daga Usman Nasidi.

WATA mata mai shekaru 73 a garin Andhra Pradesh dake kudancin kasar Indiya ta haifi tagwaye dukkaninsu mata bayan likitoci sun yi mata aiki na musamman a ranar Alhamis.

Likitan matar ya bayyana cewa mahaifiyar da tagwayen na cikin koshin lafiya.

Mangayamma Yaramati tare da mijinta wanda ke da shekaru 82 a duniya ta ce sun dade suna neman haihuwa amma Allah bai ba su ba.

“Muna matukar farin ciki da samun wannan karuwar,”
inji Sitarama Rajarao wanda shi ne mahaifin ‘yan tagwayen.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, Mista Rajarao ya samu rashin lafiyar da ta buge shi  har aka kwantar da shi a asibiti bayan kwana guda da saukar mai dakinsa.

Da yake amsa tambayar ‘yan jarida game da shekarunsu da kuma yadda rayuwar diyansu za ta kasance bisa la’akari da cewa shekarunsu sun ja, Rajarao ya ce “Babu abin da ke hannunmu dangane da rayuwar wadannan yara, duk abin da Allah ya so ya faru shi ne zai faru, don haka mun mika lamarinmu zuwa ga Allah.”

Samun wannan karuwa ya matukar faranta wa ma’aurantan rai, kasancewar sun sha tsangwama daga wurin mutanen kauyensu.

“An sha kirana da suna juya, saboda an ga ban haihu ba. Mun yi ta ganin likitoci domin neman ko akwai wani taimako da za su iya mana amma abin ya gagara.” Inji Yaramati.

Matar ta kara da cewa “Wannan shi ne lokaci mafi farin ciki a rayuwata.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here