Soji Sun Mika Wa Gwanatin Jihar Kaduna Shanu 134 Da Suka Kwato

0
377

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

RANAR Alhamis ne babban kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Birgediya Janar Jimmy Akpor, ya mika wa gwamnatin jihar Kaduna shanu 134 wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace.

Dabbobin da suka kai 134 an mika su ne ga jagoran ‘Operation Yaki’ mai ritaya, AIG Murtala Abbas a kauyen Kakau da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, dabbobin sun hada da shanu 120 da tumakai 14 wadanda jimillarsu ya kama 134. An kwato su ne daga hannun masu garkuwa da mutane da suka addabi titin Kaduna zuwa Abuja.

Aminu Mallam wanda aka fi sani da Baderi shi ne ake zargi da garkuwa da mutane. An kama shi ne a kauyen Sabon Gayan.

A ranar 2 ga watan Satumba ne, atisayen ‘Thunder Strike’ daga sojin runduna ta daya suka kai samame sansanin masu garkuwa da mutane da ke kauyukan Ligari da Sabon gayan. Bayan kwanaki kadan ne da kai samamen ne aka gano shanun a yankin Ligari.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri daban-daban wanda hakan ne ya sa ta kai samamen.

Sojin sun bayyana cewa abin takaicin da suka gano shi ne barayin shanun kan yi hayar matasan da ba su ji ba, ba su gani ba don kiwon dabbobin da suka sato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here