Matsalar Lantarki: Wajibi Kamfanonin Rarraba Hasken Lantarkin Su Kara Karfin Jarinsu

0
377

Daga Z A Sada

Har yanzu Najeriya ta gaza wajen samar da isasshen karfin wutar lantarki ga al'ummartaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

A Najeriya, duk da sayar da wani bangare na harkar wutar lantarkin kasar ga wasu kamfanoni masu zaman kansu, har yanzu al’ummar kasar na kokawa game da rashin samun wutar lantarkin yadda ya kamata.

Kwararru dai na ganin cewa matsalar ba ta rasa nasaba da rashin karfin jari na kamfanonin rarraba wutar lantarkin.

Wasu kuma na ganin cewa babbar hanyar da za a iya bi domin shawo kan matsalar ita ce a bullo da tsarin inganta karfin jarin kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOS), kamar yadda aka yi wa bankunan kasar a ‘yan shekarun da suka gabata.

Usman Mohammed, shi ne shugaban kamfanin raba wutar lantarki ga kamfanin da ke rarraba wutar ga kamfanonin da ke rarraba ta ga al’umma a Najeriya, wato TCN, kuma yana daga cikin masu cewa dole sai an dauki mataki mai kwari matukar ana son magance matsalar. Ya ce ‘Masu rarraba wuta ya kamata a ce su kara irin wannan jari, saboda su samu su gyara layukan da ba su da kyau’.

Ya kara da cewa ‘Amma idan an tafi haka, wadannan da ake da su duk sun lalace, kuma ba a da karfi da za a gyara su, to haka za mu ci gaba da kasancewa cikin matalsar wuta’.

Akwai dai kamfanonin rarraba wutar lantarki da dama a kasar ta Najeriya. Matsalar karancin wuta na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Najeriya.

Mutane da 'yan kasuwa kan yi amfani ga injina wajen sama wa kansu wutar lantarkiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Hakan ya janyo mutuwar masana’antu, da kuma dakile habbakar kananan sana’o’i.

A watan Yuli ne gwamnatin Najeriya da kamfanin Siemens na kasar Jamus suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar bunkasa samar da wutar lantarki a kasar.

A cewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yarjejeniyar za ta taimaka wajen samar da karfin wutar lantarki megawatt 7,000 nan da shekarar 2021, sannan karfin wutar zai bunkasa da megawatt 11,000 a shekara ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here