A Yau Litinin El-Rufai Na Jihar Kaduna Zai San Makomarsa

  0
  426

  Usman Nasidi, Daga Kaduna

  YAU Litinin 9 ga watan Satumba ne za a yanke hukunci a kan karar da aka shigar ta kara zaben Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna.

  Sakatariyar kotun sauraron kararrakin zabe, Hafsat Suleiman, ta bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar a garin Kaduna.

  Hafsat Suleiman ta ce kotun sauraron kararrakin zaben ta kammala zamanta ne a ranar 19 ga watan Augusta kuma ta sa ranar Litinin a matsayin ranar da za ta fidda hukuncinta a kan karar da jam’iyyar PDP ta shigar.

  Jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Ashiru, sun shigar da kara a kan zaben ranar 9 ga watan Maris tare da bukatar kotun ta soke zaben.

  Karar ta bukaci kotun da ta soke kuri’u 515,951 wadanda jam’iyyar ta ce an yi aringizonsu ne.

  Masu karar sun gabatar da shaidu 135 a cikin shaidu 685 da suka ce suna da su kuma sun zargi magudi a wajen zaben.

  Masu karar sun kara da zargar hukumar zabe mai zaman kanta da karawa El-Rufai na jam’iyyar APC kuri’u 391,741 da kuma kuri’u 124,210 ga jam’iyyar PDP.

  Sun kara da cewa, bayyana El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben ya karya doka domin ba shi ne ya ci mafi yawan kuri’u ba.

  Jam’iyyar PDP ta bakin lauyoyinta wadanda Emmanuel C. Ukala, SAN ya jagoranta, ya ce rage kuri’u 391,741 daga 1,045,427 na El-Rufai da kuma kara kuri’u 124,210 ga 814,168 na Ashiru zai maida nasara ga jam’iyyar PDP kuma Ashiru zai karbe karagar mulkin jihar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here