Super Stars Ta Kano Ta Sayo Ibrahim Iriyos Fam 10.86, Naira Dubu 5 Cur-cur

  0
  436

  Daga Z A Sada

  Ibrahim Iriyos

  BAHAUSHE na cewa,”sai shege ke raina kadan”,  kuma ”sannu ba ta hana zuwa”, mu je zuwa dai ‘yan wasan tamaula na kasashen Nahiyar Afirka inda a nahiyar akan gudanar da cinikayyar ‘yan kwallo sai dai kudin da ake sayen dan kwallo ku kusa ba ya kai wadanda ake yi a Turai.

  Sai dai hakan bai hana saye da sayar da ‘yan wasan tamaula a nahiyar ba tun daga mataki na jiha da kananan hukumomi da yankuna da unguwanni.

  Hakan ne ya sa aka gudanar da wani ciniki mafi tsada a Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu a Najeriya, inda Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin.

  Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo Ibrahin Iriyos daga Aston Villa ta Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

  Dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha’awar komawa Super Stars da murza leda ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Villa Gano.

  Hakan ya sa Iriyos kan je Super Stars atisaye a lokacin da kungiyarsa Aston Villa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake taka leda aka kuma cimma matsaya a dauko shi.

  Idin Gano shi ne shugaban Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Villa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here