Za A Yi Arangama Tsakanin ‘Yan shi’a Da ‘Yan Sanda A Gobe Talata?

0
640

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AKWAI yiwuwar za a yi mummunar arangama tsakanin mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da kungiyar shi’a da kuma rundunar ‘yan sanda yayin gabatowar tattakin tunawa da ranar Ashura a ranar Talata.

Tattakin tunawa da ranar Ashura kamar yadda kungiyar shi’a a duniya suka saba a kowace shekara, suna gudanar da shi ne a ranar 10 ga watan farko na Kalandar musulunci wato Al-Muharram.

‘Yan shi’a a fadin duniya na gudanar da wannan tattaki ne na ranar Ashura domin tunawa da mutuwar Husayn ibn Ali a yayin yakin Karbala da aka yi a kasar Iraqi a watan Oktoba na shekarar 680.

A yayin da Imam Husayn shi ne jagoran da mabiya akidar shi’a suka rika, ba bu shakka ya kasance jikan mazon tsira Annabi Muhammad (SAW).

Duk da cewar gwamnatin Najeriya ta ayyana tare da kaddamar da kungiyar a matsayin haramtacciya gami da sha ta mata layi a kan gudanar da duk wasu al’amura, kungiyar ta yi wa jami’an tsaron kasar kunnen uwar shegu da cewa babu abin da zai hana ta tattakinta a ranar Talata.

Babu shakka Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa, Muhammad Adamu, a wani sabon umarni da ya gabatar a baya-bayan nan, ya haramta kungiyar saboda zarginta da keta dokoki da kuma tayar da zaune tsaye, zargin da kungiyar ta musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here