Za Mu Tunkare Su Idan Sulhu Ya Ki Ci Ya Ki Cinyewa – Gwamna Tambuwal

0
345
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na jihar Sakkwato
Daga Z A Sada

GWAMNONIN jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina a Najeriya sun amince su yi aiki tare da takwaransu na jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar don kawo karshen matsalar tsaro.

Gwamnonin sun kudiri aniyar shawo kan bazuwar makamai da albarusai har ma da miyagun kwayoyi da satar mutane da shanu a tsakanin kasashen biyu.

Wadannan ayyuka dai sun addabi jihohin arewa maso yamma a Najeriya da ita kanta Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da na Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Muhammed Bello Matawalle na Zamfara da kuma Zakari Umaru na jihar Maradin Jamhuriyar Nijar sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron da suka shafe tsawon daren Lahadi suna gudanarwa.

Gwamna Zakari Umaru ya ce dama can dai jami’an tsaron da ke jihohin hudu na aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“Ita harka idan ta zaman lafiya ce hanyoyi iri-iri ne ya kamata a bi. Su a Sakkwato da Zamfara da Katsina sun dauki hanyar sulhu, to mu ma za mu bi wannan hanyar tare da su saboda abubuwan da ke faruwa a wajensu mu ma yana zuwa mana nan” in ji Zakari Umaru. Sai dai ya ce ba kasafai sulhu ke yi wa tufkar hanci ba.

“Wani lokaci idan an yi sulhun akwai tsagerun da ke bijire wa yarjejeniyar zaman lafiya” a cewarsa.  Amma ya ce aikin da ke gabansu shi da takwarorinsa na Najeriya shi ne yadda za su yi maganin wadannan tsagerun”.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana cewa za su ci gaba da kokarin da suke yi na yin sulhu da ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

Ya ce “za mu jawo su, wadanda za mu iya magana da su mu yi idan abu ya faskara kuma sai a tunkare su da karfin bindiga.”

Gwamnonin sun gana ne a jihar Maradi bisa gayyatar Gwamna Zakari Umaru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here