Ahmed Musa Ba Zai Buga Wasa Da Ukraine Ba

  0
  479
  Ahmed MusaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGE

  Daga Z A Sada

  TAWAGAR kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eales, za ta buga wasan sada zumunta da ta Ukraine ranar Talata.

  Wannan ne karon farko da Super Eagles za ta yi wasa tun bayan mataki na uku da ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar tsakanin watan Juni zuwa Yuli.

  Cikin wadan da Super Eagles ta je da su Masar da kuma za su buga mata wasan sada zumunta da Ukraine sun hada da mai tsaron raga Francis Uzoho da kuma Ikechukwu Ezenwa,

  Akwai kuma masu tsaron baya Olaoluwa Aina da Chidozie Awaziem da Ekong da Leon Balogun da Jamilu Collins da amsu buga tsakiya Alex Iwobi da kuma Etebo .

  Sauran sun hada da masu cin kwallo Victor Osimhen da Moses Simon da Samuel Chukwueze da Paul Onuachu da kuma Samuel Kalu.

  An kuma je Ukraine tare da mai tsaron baya Bryan Idowu da kuma Oluwasemilogo Ajayi da kuma dan kwallon Leicester City, Kelechi Iheanacho wadan da ba a je da su Masar ba.

  Sai dai kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ba zai buga karawar ba, sakamakon jinya da yake yi, bayan shi Kenneth Omeruo da Tyronne Ebuehi da Wilfred Ndidi da kuma Henry Onyekuru ba za su buga wasan ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here