Cika Kwanaki 100 Kan Mulki: Gwamna Ganduje Ya Ciri Tuta-Inji Bashir Kutama

  0
  514
  Gwamnan Jihar KANO Dakta Umar Abdullahi Ganduje

  JABIRU A HASSAN, Daga  Kano.

  SHUGABAN karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya ce a cikin kwanaki dari Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi abubuwa masu matukar amfani ga al’umma wadanda kuma za a dade ana cin moriyar su.

  Ya yi wannan bayani ne  cikin wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai, inda  ya sanar da cewa ko shakka babu jihar Kano tana amfana da ayyukan alheri daga  gwamnatin Ganduje kuma ayyuka masu nagarta bisa  la’akari da bukatun al’umma kamar  yadda ake gani a birni da yankunan karkara.

  Injiniya Bashir Kutama ya bayyana cewa a zangon farko na Gwamna Ganduje, an ga irin  managarcin ci  gaban da aka samu a fadin  jihar ta Kano, sannan dukkanin aikace-aikacen da aka yi za su ci gaba da amfanar al’umma saboda ingancin su, wanda  a cewar sa, mutanen jihar Kano suna matukar alfahari da wadannan ayyuka.

  Haka kuma shugaban karamar hukumar ta Gwarzo ya nunar da cewa da yardar Allah a zango na biyu jihar Kano za ta zamo abar misali cikin sauran jihohin wannan kasa, duk da irin kalubalen da ake fuskanta na karancin kudaden gudanar da ayyuka musamman ganin cewa Gwamna Ganduje yana da manufofi masu kyau na ciyar da jihar ta Kano gaba.

  Injiniya Kutama ya sanar da cewa yana dakyau al’umar jihar Kano su sani cewa a cikin kwanaki 100 da Ganduje ya yi bayan rantsar da shi karo na biyu, ya yi wasu  abubuwa wadanda suke da amfani kamar shirin Ruga domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma wanda shiri ne mai kyau matuka da gaske.

  Sannan ya ce Gwamna ya yi kokari kwarai da gaske wajen tabbatar da ganin ana ba da ilimin firamare da sakandire kyauta a fadin jihar Kano, wanda hakan zai taimaka sauran jihohi na arewacin Nijeriya su ma su dauka ta yadda ilimi zai bunkasa a shiyyar arewacin kasar nan kamar yadda aka kaddamar kwanan nan bisa shaidawar mataimakin shugaban kasa Osinbajo.

  Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya yi àmfani da wannan dama inda ya sanar  da cewa su ma a mataki na karamar hukuma, suna yin amfani dan abin da suke da shi wajen gudanar da ayyukan alheri ga al’ummar yankin domin samar masu da ababen more rayuwa kamar  gyaran gadoji da hanyoyi da makarantu da masallatai da kuma bunkasa kasuwanci domin bunkasa tattalin arzikin al’umma.

  A karshe, Bashir Abdullahi Kutama ya gode wa daukacin al’ummar karamar hukumar Gwarzo saboda kaunar da suke nuna masa, kana ya yaba da yadda dangantaka take tsakaninsa da ‘yan siyasar wannan yanki da kuma ma’aikatan karamar hukumar ta Gwarzo wanda a cewarsa, hakan ta sanya ake cimma nasarori a aikace.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here