Gwamnatin Kaduna Da Kasar Denmark Sun Kulla Yarjejeniyar Bude Katafaren Kamfanin Sarrafa Madara

0
506

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai a ranar Litinin 9 ga watan Satumba ya ce gwamnatinsa ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da kasar Denmark domin bunkasa sarrafa madarar shanu a jihar.

Gwamnan ya ce, an kirkiro da wannan sabon tsarin ne domin nuna wa makiyaya cewa za su iya cin moriyar dabbobinsu ta hanyar amfani da zamani, ba tare da sun rika yin zirga-zirga ba daga wuri zuwa wuri.

El-Rufa’i ya sanya hannu a kan yarjejeniyar da wani kamfanin kasar Denmark. Sunan kamfanin Arla foods international wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kamfanin, Steen Hadsdjerg.

Rahotanni sun bayyana mana cewa, idan ana maganar ayyuka ne kamfanin zai samar da ayyukan yi sama da 50, 000 inda kuma ake sa ran za a kashe Fam Miliyan €100.

A cikin jawabin da Gwamna El-Rufai ya yi ya bayyana dalilinsa na kulla wannan yarjejeniya, inda yake cewa, samar da sauki ga manoma da kuma mata wurin sarrafa madarar shanun shi ne burinsu.

Ta hanyar amfani da ire-iren wadannan kamfanoni, makiyaya za su fahimci albarkar da ke cikin kiwo da kuma hanyar cin amfaninsa cikin sauki.

“Akwai kamfanoni da yawa wadanda suka so mu kulla wannan alakar da su amma sai muka zabi Arla saboda shi ne kadai kamfanin da muke da yakinin cewa zai samar wa mutanenmu da abin da muke bukata a matsayinmu na gwamnati.” Inji El-Rufa’i.

Haka zalika, Jakadan Denmark a kasar Najeriya ya ce ofishinsa na jakadanci zai cigaba da bayar da gudunmuwa ga irin wadannan ayyuka domin ci gaban Najeriya

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here