An Damke ‘Yan Fashi Da Masu Garkuwa Da Mutane Su 6 A Yankin Toro

0
453
Matasan-da-ake-zargi-da-fashi-da-garkuwa-da-mutane-a-yankin-Toro.

Isah  Ahmed Daga Jos

RUNDUNAR kungiyar tsaro ta Danga reshen karamar hukumar Toro da ke Jihar Bauci, ta sami nasarar damke wasu matasa guda 6, da suka addabi al’ummar yankin da fashi da makami da garkuwa da mutane. Jami’an tsaron Danga sun kama wadannan matasa ne, a garin Rinji da ke wannan yanki.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari,  shugaban kungiyar ta Danga a karamar hukumar Toro, Alhaji Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa wadannan matasa guda 6, da suka addabi a al’ummar wannan yanki  da fashi da makami  da garkuwa da mutane, sun kama su ne a garin Rinji.

Ya ce wadannan matasa guda 6, sun hada da Agwom Azi da Usman Abdullahi da Jamilu Muhammad Aljan da Ayuba Bala da Ishaku Samsun da kuma Garba Yakubu Maidaji.

Ya ce sun  sami daya da bindiga da  kuma wanda yake kera bindigogin da suke amfani da su wajen aikata fashi da garkuwa da mutane.

 ‘’Wadannan matasa a duk ranakun kasuwa a wannan yanki, suna tare hanya suna yi wa mutane da suke zuwa kasuwanni fashi. Za mu mika wa babban jami’in ‘yan sanda na karamar hukumar Toro wadannan matasa, don ci gaba da bincike.

Ya yi  kira ga gwamnati da iyayen kasa su cigaba da ba su goyan baya da hadin kai, don ganin an magance wannan matsala.

Da yake zantawa da wakilinmu daya daga cikin wadannan matasa  Agwom Azi, ya bayyana cewa shi yana sana’ar walda ne a garin Rinji

Ya ce babu shakka ya hada baki da wadannan matasa inda suka zo da daddare  wani shago da yake kallon gidansu, suka yi fashi kuma suka tafi da yaran shagon guda 2 mace da namiji ‘yan kabilar ibo,  da gari ya waye ya hadu da daya daga cikin wadannan matasa,  ya ciro kudi Naira dubu 45 ya ba shi ya ce masa, nasa kason kenan.

Ya ce babu shakka ya aikata fashi da garkuwa da mutane da kuma hada baki a yi garkuwa da mutane a wannan yanki.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu wani daga cikin wadannan matasa, Usman Abdullahi ya bayyana cewa  yana zaune a garin Rinji ne. Ya ce gaskiya ne suna fashi da makami da garkuwa da mutane a wannan yanki.

‘‘Mun taba zuwa nan hanyar Agware har sau biyu mun tare mutane mun karbi kudadensu. Kuma mun taba zuwa mun fasa shaguna guda biyu mun kwashi kudade’’.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, shugaban riko na karamar hukumar Toro, Alhaji Shehu Buba Umar ya mika godiyarsa ga Allah kan wannan nasara da aka samu, na kama wadannan matasa da suke aikata fashi da garkuwa da mutane, a wannan yanki.

Ya ce ganin irin yadda wannan matsala ta garkuwa da mutane da fashi da makami ta yi kamari da kuma wannan nasara da aka samu na kama wadannan matasa, ya kira taron dukkan masu ruwa da tsaki na yankin.

 Ya ce wannan taron ya sami halartar dukkan  tsofaffin shugabannin karamar hukumar da tsofaffin kwamishinoni na yankin da sarakuna da manyan malamai, suka tattauna tare  bai wa juna shawarwari, kan wannan al’amari.

Ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da hada  kai da kungiyar tsaro ta Danga da kungiyar ‘yan banga na yankin da sauran jami’an tsaro  don magance wannan matsala.

Ya yi kira ga  sarakuna da sauran shugabanni da iyaye su tashi tsaye wajen koya wa  matasa sana’a da kokarin tabbatar da tsaro, a garuwan yankin.

Wakilinmu ya yi kokarin kiran kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauci, DSP Kamal Datti domin jin ta bakinsa, kan wannan al’amari amma bai same shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here