Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kara Kaso 2.2% A Kan Kudin Harajin Kayan Amfani

0
325

Daga Usman Nasidi.

MAJALISAR zartar wa ta tarayya (FEC) ta amince da kara kudin harajin kayan amfani (VAT) daga 5% zuwa 7.2%.

Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ga manema labarai a karshen zaman majalisar na ranar Laraba.

Sai dai, karin ba zai tabbata ba sai majalisa ta yi kwaskwarima ga dokar kara kudin haraji a kan kayan amfani wacce aka kirkira a shekarar 1994.

A shekarar 1994 ne tohon shugaban kasa a mulkin soji, Sani Abacha, ya gabatar da tsarin VAT kuma ya kai shi zuwa kaso 5%.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kara shi zuwa kaso 10% a karshen wa’adinsa na biyu da ya kare a shekarar 2007. Sai dai, tsohon shugaban kasa, marigayi Umar Musa Yar’adu, ya soke karin bayan kungiyar kwadago ta nuna adawarta a kan karin da Obasanjo ya yi.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci zaman FEC na ranar Laraba, wanda suka shafe tsawon sa’o’i 7 suna tattauna wa.

Ministar ta ce FEC ta bayar da umarni fara tuntubar gwamnotocin jihohi da kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki kafin sabon tsarin ya fara aiki a cikin shekarar 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here