Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 7 Daga Hannun Masu Garkuwa A Jihar Kaduna

0
375

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

JAMI’AN tsaro sun ceto mutum bakwai daga hannun masu garkuwa wadanda aka yi gaba da su a kan hanyar Kaduna-Abuja ranar Lahadi.

Mutanen dai sun fito ne daga Offa ta jihar Kwara inda suka nufi Kaduna a lokacin da aka sace su. Bayan kwana uku da sace mutanen sun samu sa’ar kubuta daga hannun miyagun.

Da yake karin haske a kanceto mutanen, kwamandan runudunar Operation Thunder Strike, Ibrahim Gambari ya ce wata tawaga ce mai kunshe da gamayyar dakarun soji ta ceto mutanen a kauyen Rijana dake karamar hukumar Kachia.

Kwamandan ya ce, dakarun sun samo albarusai masu tarin yawa da kuma wayoyin salula daga hannun masu garkuwar.

Ga kadan daga cikin kalaman kwamandan: “Mun kwato bindiga AK47 guda biyu, bandur din albarushi 130, wayar salula biyu, tsabar kudi N100,000 da kuma kakakin sojoji.”

Gambari ya kara da cewa za su mika da barayin zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna domin a dauki mataki mafi dacewa a game da su.

Haka zalika, ya sake cewa Operation Thunder Strike wata rundunar hadin gwiwa ce wadda ta kunshi jami’an tsaron hukumomin sojin kasa, na ruwa, na sama, ‘yan sanda, DSS da kuma NSCDC inda suke aiki tare domin magance matsalar sace-sace da kuma kashe-kashen mutane a kan hanyar Abuja-Kaduna.

“Tun daga lokacin da muka fito da wannan tsarin muna iya bakin kokarinmu wajen ganin an kawar da ire-iren wadannan munanan ayyukan dake addabar matafiya a bisa wannan babban titi.” Inji kwamandan.

Majiyarmu ta bayyana sunayen mutanen da aka ceto kamar haka: Aisha Bisola, Ahmad Abdulrafiu, Maryam Abubakar, Suleiman Kadoka, Lawal Temitope, Bala Abdullahi da Abdulrazak Okunol

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here