Isah Ahmed Daga Jos
KOTUN sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisun tarayya da ‘yan majalisun jiha da ke zama a garin Jos, fadar Jihar Filato ta yi watsi da karar da dan takarar kujerar majalisar wakilai, ta tarayya ta mazabar Mangu da Bokkos karkashin jam’iyyar APC, a zaben da ya gabata Honarabul Danjuma Haruna ya shigar. A inda yake kalubalantar nasarar da Hon arabul Solomon Maren na jam’iyyar PDP ya samu a zaben, saboda rashin kawo kwararan shaidu. Kotun ta yi watsi da karar ne, a zaman da ta yi a ranar Litinin din nan da ta gabata.
Da yake yanke hukumcin shugaban kotun Mai shari’a N.T. Ezeogwu ya bayyana cewa masu karar sun kasa gabatar wa kotun cikakkun shaidu, kan zargin da suke yi na aringizon kuru’u tare da saba qa’idojin zabe a lokacin da aka gudanar da zaben.
Mai shari’ar ya ce bayan da kotun tayi nazarin wannan kara, sai ta gano cewa masu karar ba su da cikakkun shedu kan wannan kara da suke yi.
Ya ce masu karar sun kasa kawowa kotun akwatunan zaben tare takardun zaben da za su tabbatar cewa an aikata laifin da suke zargin an aikata.
Mai shari’ar ya yi bayanin cewa shedu guda 31 da masu karar suka gabatar, basu tabbatar da laifin da ake zargin an aikata ba. Don haka kotun ta yi watsi da wannan kara.