Sana’ar Nika Ta Yi Mani Daidai-Rukayya Ahmed

  0
  627
  Rukayya Ahmed

  Isah  Ahmed Daga Jos

  WATA yarinya ‘yar shekara 10 da haihuwa mai suna Rukayya Ahmed, da take gudanar da sana’ar nika garin masara da dawa a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, ta bayyana cewa wannan sana’a ta nika gari, ta yi mata daidai. Rukayya Ahmed ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu.

  Ta ce babanta ne ya koya mata wannan sana’a tun tana karama. Ta ce a yanzu tana yin wannan sana’a ita kadai da kanta, ta tayar da injin tayi aikin nikan, kuma idan injin ya lalace ta kwace shi ta gyara, sannan ta tayar ta ci gaba da aiki.

  ‘’Babana ya kan yi tafiya ya bar ni da injin, ya yi kwana da kwanaki ya dawo ya samu, babu wata matsala. A duk rana nakan yi  aikin N1,500 wata rana N2,000 wata rana har Naira N3,000 nake yi’’.

  Rukayya Ahmed ta yi bayanin cewa  duk da wannan sana’a da take, yi tana zuwa makarantar firamare domin a yanzu tana aji hudu na makarantar firamare. Kuma idan lokacin tafiya makaranta ya yi, takan rufe ta tafi idan an taso ta zo ta sake budewa ta ci gaba da aiki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here