‘Yan Sandan A Filato Sun Damke Mata 5 Da Ake Zargi Da Fataucin Yara

0
717
Matan da ake zargi da fataucin kananan yara tare da wasu da ake zargi da aikata laifuffuka.

Isah  Ahmed Daga  Jos

RUNDUNAR ‘yan sandan  Jihar Filato ta sami nasarar damke wasu mata guda 5, da ake zargi da aikata laifin fataucin kananan yara. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista  Isaac Akinmoyede ne ya bayyana haka, lokacin da yake gabatar wa ‘yan jarida wadannan mata, a hedkwatar rundunar da ke garin Jos.

Kwamishinan ya bayyana sunayen wadannan mata da ake zargi, kamar haka   Rose Adams ‘yar shekara 25 da Mildred Bakwo ‘yar shekara 34 da Lisa Yisa Yelkopba ‘yar shekara 35 da Fatima Abdul ‘yar shekara 20 da kuma Christiana Ochuba ‘yar shekara 32.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa a ranar 23 ga watan Augustan da ya gabata ne, wani mutum mai suna Chidi Daniel da ke zaune ne a unguwar Jenta Mangoro a garin Jos. Ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na A Division cewa a ranar 31 ga watan yulin da ya gabata, matarsa mai suna Rose Adams ta bar gidansa da ke garin Dadin kowa, a karamar hukumar Jos ta kudu tare da yaranta guda 2 Chinedu Daniel dan shekara 1 da wata 8, da Chubuike Daniel dan shekara 1 da haihuwa.

‘’Mai karar ya yi bayanin cewa matar tasa ta dawo gida a ranar 23 ga watan Augusta da Chinedu Daniel kadai, ba tare da daya dan uwan nasa, Chibuike Daniel ba. Lokacin da ya tambaye ta, ina ta bar Chibuike Daniel?  sai ta ce masa ta bayar da shi ga wata mata, da take aiki a wata gidauniyar kula da kananan yara’’.

Kwamishinan ya ce amma da ‘yan sanda suka ci gaba da bincike, sai suka gano cewa wannan mata ta sayar da dan nata ne, ga wata mata mai suna Christiana Ochuba da ke zaune a hanyar Rukubu da ke garin Jos.

Kwamishinan ya ce  da suka ci gaba da bincike ne, sai suka kai ga kama sauran  matan  da ake zargi da fataucin yara.

Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincikenta za ta gurfanar da wadannan mata a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here